Laraba 23 Satumba 2026 - 21:20
An Gudanar da Jana’izar Ayatullahil Uzma Shubairi Zanjani a Qum + Hotuna da Bidiyo

Hauza/ An gudanar da taron jana’izar Ayatullahil Uzma Shubairi Zanjani daga Masallacin Makarantar Imam Khumaini (RA), da ke Dandalin Jihad zuwa Haramin Sayyida Ma'asuma (S) a birnin Qum.

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, an  gudanar da taron jana’izar Ayatullahil Uzma Shubairi Zanjani daga Masallacin Makarantar Imam Khumaini (RA), da ke Dandalin Jihad zuwa Haramin Sayyida Fatima Ma'asuma (S) a birnin Qum. An samu halartar dimbin wakilan gidajen Maraji’an Taklidi, malamai, malaman Hauza, ɗaliban Hauza da kuma al’umma daga sassa daban-daban.

A cewar rahoton, a wannan taro an samu gagarumar halartar wakilan gidajen Maraji’an Taklidi, fitattun malaman Hauza, jami’an gwamnati da na soji. Haka kuma, al’umma daga sassa daban-daban sun fito domin yin bankwana da wannan babban Marja’i, inda suka cika hanyar da ake gudanar da jana’izar.

A yayin jana'izar da kuma bankwana, an ɗauki gawar marigayin daga Dandalin Jihad, ta bi ta titin 19 Dey zuwa Haramin Mai Tsarki na Sayyida Ma’asuma (S), inda aka binne shi a cikin wannan Harami mai tsarki.

An Gudanar da Jana’izar Ayatullahil Uzma Shubairi Zanjani a Qum + Hotuna da Bidiyo

An Gudanar da Jana’izar Ayatullahil Uzma Shubairi Zanjani a Qum + Hotuna da Bidiyo

An Gudanar da Jana’izar Ayatullahil Uzma Shubairi Zanjani a Qum + Hotuna da Bidiyo

An Gudanar da Jana’izar Ayatullahil Uzma Shubairi Zanjani a Qum + Hotuna da Bidiyo

An Gudanar da Jana’izar Ayatullahil Uzma Shubairi Zanjani a Qum + Hotuna da Bidiyo

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha